caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu At-Tawba, aya 114

Madina · tsarin saukarwa 113 · 9:114

وَمَا كَانَ ٱسْتِغْفَارُ إِبْرَٰهِيمَ لِأَبِيهِ إِلَّا عَن مَّوْعِدَةٍ وَعَدَهَآ إِيَّاهُ فَلَمَّا تَبَيَّنَ لَهُۥٓ أَنَّهُۥ عَدُوٌّ لِّلَّهِ تَبَرَّأَ مِنْهُ إِنَّ إِبْرَٰهِيمَ لَأَوَّٰهٌ حَلِيمٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma istigifãrin Ibrãhĩm ga ubansa bai kasance ba fãce sabõda wani wa'adi ne da ya ƙulla alƙawarinsa da shi, sa'an nan a lõkacin da ya bayyana a gare shi (Ibrãhĩm) cẽwa lalle ne shĩ (ubansa) maƙiyi ne ga Allah, sai ya barranta daga gare shi. Lalle ne Ibrahim, haƙĩƙa, mai yawan addu'a ne, mai haƙuri.
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70