خُذْ مِنْ أَمْوَٰلِهِمْ صَدَقَةً تُطَهِّرُهُمْ وَتُزَكِّيهِم بِهَا وَصَلِّ عَلَيْهِمْ إِنَّ صَلَوٰتَكَ سَكَنٌ لَّهُمْ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa karɓi sadaka daga dũkiyõyinsu kana tsarkake su, kuma kana tabbatar da kirkinsu da ita. Kuma ka yi musu addu'a. Lallai addu'õ'inKa natsuwã ne a gare su. Kuma Allah ne Mai ji, Masani.