caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Al-A'raaf, aya 73

Makka · tsarin saukarwa 39 · 7:73

وَإِلَىٰ ثَمُودَ أَخَاهُمْ صَٰلِحًا قَالَ يَٰقَوْمِ ٱعْبُدُوا۟ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنْ إِلَٰهٍ غَيْرُهُۥ قَدْ جَآءَتْكُم بَيِّنَةٌ مِّن رَّبِّكُمْ هَٰذِهِۦ نَاقَةُ ٱللَّهِ لَكُمْ ءَايَةً فَذَرُوهَا تَأْكُلْ فِىٓ أَرْضِ ٱللَّهِ وَلَا تَمَسُّوهَا بِسُوٓءٍ فَيَأْخُذَكُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma zuwa ga Samũdãwa ɗan'uwansu, Sãlihu, ya ce: "Yã mutãnena! Ku bauta wa Allah; bã ku da wani abin bauta wa wanninSa. Haƙĩƙa hujja bayyananniya tã zo muku daga Ubangijinku! wannan rãƙumar Allah ce, a gare ku, wata ãyã ce. Sai ku bar ta ta ci, a cikin ƙasar Allah, kuma kada ku shãfe ta da wata cũta har azãba mai raɗaɗi ta kãmã ku."
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70