قُلْ إِنِّى عَلَىٰ بَيِّنَةٍ مِّن رَّبِّى وَكَذَّبْتُم بِهِۦ مَا عِندِى مَا تَسْتَعْجِلُونَ بِهِۦٓ إِنِ ٱلْحُكْمُ إِلَّا لِلَّهِ يَقُصُّ ٱلْحَقَّ وَهُوَ خَيْرُ ٱلْفَٰصِلِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Lalle ne inã kan hujja daga Ubangjina, kuma kun ƙaryata (ni) game da Shi; abin da kuke nẽman gaugãwarsa, bã ya wurina, hukunci kuwa bai zama ba fãce, ga Allah, Yanã bãyar da lãbãrin gaskiya, kuma shĩ ne mafi alhẽrin mãsu rarrabẽwa."