إِنَّ ٱلَّذِينَ يُحَآدُّونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ كُبِتُوا۟ كَمَا كُبِتَ ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ وَقَدْ أَنزَلْنَآ ءَايَٰتٍۭ بَيِّنَٰتٍ وَلِلْكَٰفِرِينَ عَذَابٌ مُّهِينٌ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle waɗanda ke sãɓã wa Allah da ManzonSa, an wulãkanta su kamar yadda aka wulãkantar da waɗanda ke a gabãninsu, kuma lalle Mun saukar da ãyõyi bayyanannu, kuma kãfirai nã da azãba mai wulãkantãwa.