وَإِذْ أَوْحَيْتُ إِلَى ٱلْحَوَارِيِّـۧنَ أَنْ ءَامِنُوا۟ بِى وَبِرَسُولِى قَالُوٓا۟ ءَامَنَّا وَٱشْهَدْ بِأَنَّنَا مُسْلِمُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Kuma a lõkacin da Na yi wahayi zuwa ga Hawãriyãwa[1] cewa ku yi ĩmãni da Ni, kuma da Manzo Na. Suka ce: "Mun yi ĩmãni, kuma ka shaida da cewa lalle mu, mãsu sallamãwa ne."