وَقَالُوٓا۟ ءَأَٰلِهَتُنَا خَيْرٌ أَمْ هُوَ مَا ضَرَبُوهُ لَكَ إِلَّا جَدَلًۢا بَلْ هُمْ قَوْمٌ خَصِمُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma suka ce: "Shin, gumãkanmu ne mafĩfĩta kõ shi (¦an Maryama)?" Ba su buga wannan misãli ba a gare ka fãce dõmin yin jidãli.[1] Ã'a, sũ mutãne nemãsu husũma.