إِن تَدْعُوهُمْ لَا يَسْمَعُوا۟ دُعَآءَكُمْ وَلَوْ سَمِعُوا۟ مَا ٱسْتَجَابُوا۟ لَكُمْ وَيَوْمَ ٱلْقِيَٰمَةِ يَكْفُرُونَ بِشِرْكِكُمْ وَلَا يُنَبِّئُكَ مِثْلُ خَبِيرٍ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiIdan kun kira su, bã zã su ji kiranku ba, kuma kõ sun jiya, bã zã su karɓa muku ba, kuma a Rãnar ¡iyãma zã su kãfirce wa shirkinku, kuma bãbu mai bã ka lãbãri, kamar wanda ya sani.