وَلَمَّا رَءَا ٱلْمُؤْمِنُونَ ٱلْأَحْزَابَ قَالُوا۟ هَٰذَا مَا وَعَدَنَا ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥ وَصَدَقَ ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥ وَمَا زَادَهُمْ إِلَّآ إِيمَٰنًا وَتَسْلِيمًا
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma a lõkacin da mũminai suka ga ƙungiyõyin kãfirai, sai suka ce, "Wannan ne abin da Allah da Manzon Sa suka yi mana wa'adi, Allah da Manzon Sa sunyi gaskiya." Kuma wannan bai ƙãra musu kõme ba fãce ĩmãni da sallamãwa.