أَلَمْ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ نَصِيبًا مِّنَ ٱلْكِتَٰبِ يُدْعَوْنَ إِلَىٰ كِتَٰبِ ٱللَّهِ لِيَحْكُمَ بَيْنَهُمْ ثُمَّ يَتَوَلَّىٰ فَرِيقٌ مِّنْهُمْ وَهُم مُّعْرِضُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, ba ka ga waɗanda aka bai wa rabo daga littãfi ba ana kiran su zuwa ga Littãfin Allah dõmin ya yi hukunci a tsakãninsu sa'an nan wata ƙungiya daga cikinsu ta jũya bãya, kuma sunã mãsu bijirẽwa?