فَإِذَا رَكِبُوا۟ فِى ٱلْفُلْكِ دَعَوُا۟ ٱللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ فَلَمَّا نَجَّىٰهُمْ إِلَى ٱلْبَرِّ إِذَا هُمْ يُشْرِكُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, a lõkacin da suka shiga cikin jirgin ruwa, sun kirãyi Allah sunã mãsu tsarkake addini a gare shi, to, a lõkacin da Ya tsĩrar da su zuwa ga tudun ƙasã, sai gã su sunã shirki.