caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Ibrahim, aya 23

Makka · tsarin saukarwa 72 · 14:23

وَأُدْخِلَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّٰلِحَٰتِ جَنَّٰتٍ تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَا بِإِذْنِ رَبِّهِمْ تَحِيَّتُهُمْ فِيهَا سَلَٰمٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma aka shigar da waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, a gidãjen Aljanna, kõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu sunã madawwamã a cikinsu da iznin Ubangijinsu, gaisuwarsu a cikinta "Salãm", (wãtau Aminci).
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70