يُوسُفُ أَيُّهَا ٱلصِّدِّيقُ أَفْتِنَا فِى سَبْعِ بَقَرَٰتٍ سِمَانٍ يَأْكُلُهُنَّ سَبْعٌ عِجَافٌ وَسَبْعِ سُنۢبُلَٰتٍ خُضْرٍ وَأُخَرَ يَابِسَٰتٍ لَّعَلِّىٓ أَرْجِعُ إِلَى ٱلنَّاسِ لَعَلَّهُمْ يَعْلَمُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Yã Yũsufu! Yã kai mai yawan gaskiya! Ka yi mana fatawa a cikin shãnu bakwai mãsu ƙiba, waɗansu bakwai rãmammu sunã cin su, da zangarku bakwai kõrãye da waɗansu ƙẽƙasassu, tsammãnĩna in kõma ga mutãne, tsammãninsu zã su sani."