قَالَ تَزْرَعُونَ سَبْعَ سِنِينَ دَأَبًا فَمَا حَصَدتُّمْ فَذَرُوهُ فِى سُنۢبُلِهِۦٓ إِلَّا قَلِيلًا مِّمَّا تَأْكُلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa ce: "Kunã shũka, shẽkara bakwai tutur, sa'an nan abin da kuka girbe, sai ku bar shi, a cikin zanganniyarsa,[1] sai kaɗan daga abin da kuke ci."