أَلَآ إِنَّهُمْ يَثْنُونَ صُدُورَهُمْ لِيَسْتَخْفُوا۟ مِنْهُ أَلَا حِينَ يَسْتَغْشُونَ ثِيَابَهُمْ يَعْلَمُ مَا يُسِرُّونَ وَمَا يُعْلِنُونَ إِنَّهُۥ عَلِيمٌۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, lalle sũ sunã karkatar[1] da ƙirjinsu dõmin su ɓõye daga gare shi. To, a lõkacin da suke lulluɓẽwa da tufãfinsu Yanã sanin abin da suke ɓoyewa da abin da suke bayyanãwa. Lalle Shi Masani ne ga abin da yake a cikin ƙirãzã.