فَلَا تَكُ فِى مِرْيَةٍ مِّمَّا يَعْبُدُ هَٰٓؤُلَآءِ مَا يَعْبُدُونَ إِلَّا كَمَا يَعْبُدُ ءَابَآؤُهُم مِّن قَبْلُ وَإِنَّا لَمُوَفُّوهُمْ نَصِيبَهُمْ غَيْرَ مَنقُوصٍ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda haka kada ka kasance a cikin shakka daga abin da waɗannan suke bautawa. Bã su wata ibãda fãce kamar yadda ubanninsu ke aikatãwa a gabani. Kuma haƙĩƙa Mũ, Mãsu cika musu rabon su ne, bã tãre da nakasãwa ba.