بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ الٓر كِتَٰبٌ أُحْكِمَتْ ءَايَٰتُهُۥ ثُمَّ فُصِّلَتْ مِن لَّدُنْ حَكِيمٍ خَبِيرٍ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiA. L̃.R. Littãfi ne an kyautata ãyõyin sa, sa'an nan an bayyanã su daki-daki, daga wurin Mai hikima, Mai ƙididdigewa.