caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu At-Tawba, aya 35

Madina · tsarin saukarwa 113 · 9:35

يَوْمَ يُحْمَىٰ عَلَيْهَا فِى نَارِ جَهَنَّمَ فَتُكْوَىٰ بِهَا جِبَاهُهُمْ وَجُنُوبُهُمْ وَظُهُورُهُمْ هَٰذَا مَا كَنَزْتُمْ لِأَنفُسِكُمْ فَذُوقُوا۟ مَا كُنتُمْ تَكْنِزُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA Rãnar da ake ƙõna shi a kanta a cikin wutar Jahannama, sai a yi lalas da ita ga gõshinansu da sãshinansu da bãyayyakinsu, (a ce musu): "Wannan ne abin da kuka taskace dõmin rãyukanku. To, ku ɗanɗani abin da kuka kasance kunã sanyãwa a taska."
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70