وَمِمَّنْ حَوْلَكُم مِّنَ ٱلْأَعْرَابِ مُنَٰفِقُونَ وَمِنْ أَهْلِ ٱلْمَدِينَةِ مَرَدُوا۟ عَلَى ٱلنِّفَاقِ لَا تَعْلَمُهُمْ نَحْنُ نَعْلَمُهُمْ سَنُعَذِّبُهُم مَّرَّتَيْنِ ثُمَّ يُرَدُّونَ إِلَىٰ عَذَابٍ عَظِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma daga waɗanda suke a gẽfenku daga ƙauyãwa akwai munãfukai,[1] haka kuma daga mutãnen Madnĩa. Sun gõge a kan munãfunci, bã ka sanin su, Mũ ne Muke sanin su. zã Mu yi musu azãba sau biyu, sa'an nan a mayar da su zuwa ga azãba mai girma.