وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَهَاجَرُوا۟ وَجَٰهَدُوا۟ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱلَّذِينَ ءَاوَوا۟ وَّنَصَرُوٓا۟ أُو۟لَٰٓئِكَ هُمُ ٱلْمُؤْمِنُونَ حَقًّا لَّهُم مَّغْفِرَةٌ وَرِزْقٌ كَرِيمٌ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka yi hijira, kuma suka yi Jihãdi, a cikin hanyar Allah, kuma da waɗanda suka bãyar da masauki, kuma suka yi tamiako, waɗannan sũ ne mũminai da gaskiya, sunãda gãfara da wani Abinci na karamci.