وَإِذَا سَمِعُوا۟ مَآ أُنزِلَ إِلَى ٱلرَّسُولِ تَرَىٰٓ أَعْيُنَهُمْ تَفِيضُ مِنَ ٱلدَّمْعِ مِمَّا عَرَفُوا۟ مِنَ ٱلْحَقِّ يَقُولُونَ رَبَّنَآ ءَامَنَّا فَٱكْتُبْنَا مَعَ ٱلشَّٰهِدِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan suka ji abin da aka saukar zuwa ga Manzo, kanã ganin idanunsu sunã zubar da hawãye, sabõda abin da suka sani daga gaskiya, sunã cewa: "Yã Ubangijinmu! Mun yi ĩmãni, sai ka rubuta mu tãre da mãsu shaida.