قَالُوا۟ يَٰقَوْمَنَآ إِنَّا سَمِعْنَا كِتَٰبًا أُنزِلَ مِنۢ بَعْدِ مُوسَىٰ مُصَدِّقًا لِّمَا بَيْنَ يَدَيْهِ يَهْدِىٓ إِلَى ٱلْحَقِّ وَإِلَىٰ طَرِيقٍ مُّسْتَقِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSuka ce: "Ya mutãnenmu! Lalle mũ, mun ji wani littãfi an saukar da shi a bãyãn Mũsã, mai gaskatãwa ga abin da ke a gaba da shi, yanã shiryarwa ga gaskiya da kuma zuwa ga hanya madaidaiciya.