فَقَٰتِلْ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ لَا تُكَلَّفُ إِلَّا نَفْسَكَ وَحَرِّضِ ٱلْمُؤْمِنِينَ عَسَى ٱللَّهُ أَن يَكُفَّ بَأْسَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ وَٱللَّهُ أَشَدُّ بَأْسًا وَأَشَدُّ تَنكِيلًا
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda haka, ka[1] yi yãƙi a cikin hanyar Allah, ba a kallafa maka ba, face a kanka, kuma ka kwaɗaitar da mũminai. Akwai tsammãnin Allah Ya kange gãfin waɗanda suka kãfirta, kuma Allah ne Mafi tsananin gãfi, kuma Mafi tsananin azabtãwa.