يَسْتَخْفُونَ مِنَ ٱلنَّاسِ وَلَا يَسْتَخْفُونَ مِنَ ٱللَّهِ وَهُوَ مَعَهُمْ إِذْ يُبَيِّتُونَ مَا لَا يَرْضَىٰ مِنَ ٱلْقَوْلِ وَكَانَ ٱللَّهُ بِمَا يَعْمَلُونَ مُحِيطًا
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSuna nẽman ɓõyewa daga mutãne kuma bã su nẽmanɓõyewa daga Allah, alhãli kuwa Shi Yana tãre da su a lõkacin da suke kwãna da niyyar yin abin da bã Ya yarda da shi daga maganar. Kuma Allah Yã kasance ga abin da suke aikatãwa Mai kẽwayẽwa.