وَإِذْ فَرَقْنَا بِكُمُ ٱلْبَحْرَ فَأَنجَيْنَٰكُمْ وَأَغْرَقْنَآ ءَالَ فِرْعَوْنَ وَأَنتُمْ تَنظُرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma a lõkacin da Muka raba tẽku sabõda ku, sai Muka tsĩrar da ku kuma Muka nutsar da mutãnen Fir'auna, alhãli kuwa kũ kuna kallo.