قُلْ هَٰذِهِۦ سَبِيلِىٓ أَدْعُوٓا۟ إِلَى ٱللَّهِ عَلَىٰ بَصِيرَةٍ أَنَا۠ وَمَنِ ٱتَّبَعَنِى وَسُبْحَٰنَ ٱللَّهِ وَمَآ أَنَا۠ مِنَ ٱلْمُشْرِكِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Wannan ce hanyãta;[1] inã kira zuwa ga Allah a kan basĩra, nĩ da waɗanda suka bĩ ni, kuma tsarki ya tabbata ga Allah! Nĩ kuma, ban zama daga mãsu shirki ba."