وَإِلَىٰ عَادٍ أَخَاهُمْ هُودًا قَالَ يَٰقَوْمِ ٱعْبُدُوا۟ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنْ إِلَٰهٍ غَيْرُهُۥٓ إِنْ أَنتُمْ إِلَّا مُفْتَرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma zuwa ga Ãdãwa, (Mun aika) ɗan'uwansu Hũdu. Ya ce: "Yã kũ mutãnena! Ku bauta wa Allah. Ba ku da wani abin bautãwa fãce Shi. Ba ku kasance ba fãce kunã mãsu ƙirƙirãwa.