وَلَا تُعْجِبْكَ أَمْوَٰلُهُمْ وَأَوْلَٰدُهُمْ إِنَّمَا يُرِيدُ ٱللَّهُ أَن يُعَذِّبَهُم بِهَا فِى ٱلدُّنْيَا وَتَزْهَقَ أَنفُسُهُمْ وَهُمْ كَٰفِرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma kada dũkiyõyinsu da ɗiyansu su bã ka sha'awa. Abin sani kawai, Allah Yanã nufin Ya yi musu azãba da su a cikin dũniya, kuma rãyukansu su fita alhãli kuwa sunã kãfirai.