لَا يَسْتَـْٔذِنُكَ ٱلَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلْيَوْمِ ٱلْـَٔاخِرِ أَن يُجَٰهِدُوا۟ بِأَمْوَٰلِهِمْ وَأَنفُسِهِمْ وَٱللَّهُ عَلِيمٌۢ بِٱلْمُتَّقِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗanda suke yin ĩmãnida Allah da Rãnar Lãhira, bã zã su nẽmi izininka ga yin, jihãdida dũkiyõyinsu da rãyukansu ba. Kuma Allah ne Masani ga mãsu taƙawa.