ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ لَهُمْ عَذَابٌ شَدِيدٌ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّٰلِحَٰتِ لَهُم مَّغْفِرَةٌ وَأَجْرٌ كَبِيرٌ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗanda suka kãfirta suna da azãba mai tsanani kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wata gãfara da sakamako mai girma.