إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ لَن تُغْنِىَ عَنْهُمْ أَمْوَٰلُهُمْ وَلَآ أَوْلَٰدُهُم مِّنَ ٱللَّهِ شَيْـًٔا وَأُو۟لَٰٓئِكَ أَصْحَٰبُ ٱلنَّارِ هُمْ فِيهَا خَٰلِدُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne waɗanda suka kãfirta, dũkiyõyinsu kõ ɗiyansu bã zã su wadatar musu da kõme ba daga Allah kuma waɗannan abõkan wuta ne, sũ, acikinta, madawwama ne.