caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Ar-Ra'd, aya 11

Madina · tsarin saukarwa 96 · 13:11

لَهُۥ مُعَقِّبَٰتٌ مِّنۢ بَيْنِ يَدَيْهِ وَمِنْ خَلْفِهِۦ يَحْفَظُونَهُۥ مِنْ أَمْرِ ٱللَّهِ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُغَيِّرُ مَا بِقَوْمٍ حَتَّىٰ يُغَيِّرُوا۟ مَا بِأَنفُسِهِمْ وَإِذَآ أَرَادَ ٱللَّهُ بِقَوْمٍ سُوٓءًا فَلَا مَرَدَّ لَهُۥ وَمَا لَهُم مِّن دُونِهِۦ مِن وَالٍ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi(Kowannenku) Yanã da waɗansu malã'iku mãsu maye wa jũna a gaba gare shi da bãya gare shi, sunã tsare shi daga umurnin Allah. Lalle ne Allah bã Ya canja abin da yake ga, mutãne sai sun canja abin da yake ga zukatansu. Kuma idan Allah Ya yi nufin wata azãba game da mutãne, to, bãbu mai mayar da ita, kuma bã su da wani majiɓinci[1] baicin Shi.
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70